Gwamanan Zamfara Matawalle Ya Biya Miliyan 100 ga Dalibai Masu Rubuta WAEC
Bello Matawallen Maradun ya amince da biyan zunzurutun kudade kimanin miliyan 100 ga daliban jihar Zamfara don su rubuta jarabawar WAEC.
KARANTA:- Dan Wasan Fim na Nollywood ya kammala Digirinsa na Biyu
Kudaden za’a damkawa ofishin jarabawar WAEC din domin samun damar rubuta jarabawar WAEC ga dukkan daliban dake jihar Zamfara.
Jamilu Iliyasu Sakataren gwamna na dindindin ya bayyana hakane a wani bayani da yakeyi yace biyan kudin jarabawar na daga cikin yun kurin gwamna wajan kawo cigaban karatu a Jahar da gwamna keyi.
Yace gwamnatin Zamfara a shirye take tsaf zakuma tayi iya yinta don ganin daliban jihar sun samu sakamako Mai kyau.
Gwamanan Bello Matawallen Maradun ya nuna farincikinsa ga hukumar Ilimi ta tarayya da Kuma cibiyar WAEC da irin taimako da sukewa Ilimi a jahar.
Ya Kara bayyana jindadinsa ga gwamanatin tarayya domin ciyar da Ilimin a Jihar da takeyi.
Gwmana Matawalle yasha alwashin cigaba da taimakawa fanni Ilimi dakuma matasa masu tasowa domin cimma burinsu na Ilimi.
Comments 1