Daga Bashir Abdullahi El-bash:-
A cigaba da nade-naden muƙaman da ya ke yi tun bayan shiga Ofishin gwamna a wa’adin zangon mulki na biyu, a wannan rana Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano, ya amince da naɗa Shugaban kungiyar wasan ƙwallon ƙafa ta (Kano Pillars) da sakataren hukumar ba da tallafin karatu ta Jiha da kuma sakataren hukumar kula da harkokin lafiya mai zaman kanta.
Sauran sun hada da: daraktan ma’aikatar samar da ruwan sha ((RUWASA), da shugaban kamfanin ma’aikatar samar da wutar lantarki ta Jihar Kano (KHEDCO) da kuma shugaban ma’aikatar inganta harkokin noma (RAAMP) sai kuma manajan daraktan kasuwanni.
Jerin mutanen da kuma ma’aikatun da aka ba su sun hada da:
1. Injiniya Hadiza Ahmed Tukur, manajan daraktar: Kano Hydro Electricity Development Company (KHEDCO).
2. Dakta Usman Tijjani, sakataren hukumar, Private Health Institutions Management Agency (PHIMA).
3. Alhaji Uba Zubairu, manajan daraktan kasuwar: Muhammadu Abubakar Rimi (Sabon Gari).
4. Yahaya Adamu Garin Ali, manajan daraktan: Rural Access & Agricultural Mobility Project (RAAMP).
5. Onarabul Abubakar Zakari Muhammad, sakataren Kano State Scholarship Board.
6. Dakta, Yusuf Mohammed Sabo, manajan daraktan Consumer Protection Council.
7. Alhaji Abba Muhammad Bello, manajan daraktan kasuwar kantin kwari.
8. Ibrahim Salisu Bichi, manajan daraktan Rural Water Supply Agency (RUWASA).
9. Alhaji Surajo Shu’aibu Yahaya, Shugaban kungiyar Kano Pillars.
Wannan nadi nasu ya fara aiki ne nan take. Kana kuma gwamna Ganduje ya bayyana cewa an zabo su ne la’akari da tarihin kwazon aikinsu a baya, dan haka ne ma ya hore su da su zama masu himma da kwazo gami da tafiya da zamani kan aiki da harkokin fasahar zamani dangane da wadannan ayyuka da aka ba su. Domin Duniyar yanzu ta na tafiya ne da ayyukan fasahar zamani wato (Takanologi).