Gwamna Abdulrazaq ya koka kan yawaitar ta’addanci a Jihar
Gwamna Abdulrahaman Abdulrazaq na jihar Kwara, a ranar Laraba, ya bayyana damuwarsa kan yawaitar hare-haren ‘yan bindiga, garkuwa da mutane da rikicin makiyaya/manoma.
Da yake jawabi a lokacin da sabon kwamandan hukumar tsaro ta farin kaya ta Najeriya NSCDC, Muhammed Tukur Ibrahim, ya kai masa ziyarar ban girma a gidan gwamnati dake Ilorin, gwamnan ya bukaci sabon kwamandan da ya kara hada kai don yakar matsalolin da ke samun jihar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ba kada mahimmanci a siyasance, ka janyo wa PDP shan kaye a 2015 – Wike ga Lamido
Ya yi alkawarin mutunta bukatun rundunar tsaron.
Gwamna Abdulrazaq, ya bukaci kwamandan da ya ci gaba da yin ƙoƙari tare da tabbatar da sauke nauyin dake wuyan sa a fannin samar da tsaro a jihar.
Kwamandan Tukur, tun da farko ya yabawa gwamnan bisa goyon bayan da yake baiwa jami’an tsaro da sadaukar da kai ga jihar.
Ya yi alkawarin hada kai da sauran hukumomin tsaro wajen yaki da matsalar ‘yan fashi da ta’addanci da garkuwa da mutane da kuma laifukan da suka shafi muggan kwayoyi.
Kwamandan, ya kuma bukaci a kara tallafa wa rundunar musamman a bangaren kayan aiki da kuma ofishin dindindin na rundunar.
A WANI LABARIN KUMA: Yanzu-Yanzu: Hukumar EFCC Ta Kama Akantan Hukumar NDDC Kan Badakalar Naira Billiyan 25