Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo ya nada dansa Babajide a matsayin Darakta-Janar na sashin lura da ayyuka da aiwatarwa (PPIMU).
An sanar da nadin dan gwamnan tare da na kwamishinoni 14.
Kwamishinan yada labarai da wayar da kan jama’a, Donald Ojogo ne ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Talata.
“Gwamnan jihar Ondo, Arakunrin Oluwarotimi Akeredolu, SAN, ya nada sabbin kwamishinoni 14 da masu ba da shawara na musamman guda bakwai.”
“Wadanda aka nada kwamishinan sune kamar haka: Mrs Bamidele Ademola Olateju (Akoko South East), Otunba Adefarati Gboyega (Akoko South West), Rt Hon Olotu Fatai (Akoko North East), Dr. Julianah Oshadahun (Akoko North West), Otunba Dele Ologun. (Akure North), Mr. Sunday Adekunle (Idanre) da Engr. Razaq Obe (Ifedore).
KARANTA WANNAN LABARIN : An kashe wata Uwa da Danta Mai shekara 2
“Sauran su ne Dr. Banji Awolowo Ajaka (Ilaje), Fasto Emmanuel Igbasan (Irele), Mrs Yetunde Adeyanju (Odigbo), Mista Femi Agagu (Okitipupa), Hon. Akinlosotu (Ondo East), Hon Omolola Fagbemi (Ondo West) da Cif Olayato Aribo (Ose).
“Wadanda aka zaba a matsayin masu ba da shawara na musamman sun hada da: Cif (Dr) Victor Ategbole, Dr. (Mrs) Wunmi Egbayelo Ilawole, Hon. (Barr) Tobi Ogunleye Felix, Dr. Ajibayo Adeyeye, Mrs Olamide Falana, Dr. Francis Adedayo Faduyile da Mr Oyeniyi Oseni.”
“Za a mika sunayen wadanda aka nada, musamman mukamin kwamishina zuwa majalisar dokoki domin tantancewa.”
“Duk wadanda aka zaba/ za a rantsar da su ne bayan Yan majalissun jihar sun I matakan da suka dace na majalisa. Gwamna yana yi wa duk wadanda aka zaba fatan alheri.”
A bara, Akeredolu ya yi takama da cewa zai iya nada dansa a matsayin shugaban ma’aikata kuma babu abin da zai hana.