Gwamnan Jihar Borno Babagana Umara Zulum ya jagoranci maido da wasu yan gudun hijira izuwa wasu kananan hukumomi biyar a Jihar.
Yan gudun da suka shafe shekara bakwai a sansanin yan gudun hijira na Gubio duk an maida su kananan hukumominsu da suka hada da Kukawa da Marte da Bama da Gwoza gami da Ngala.
Babagana Zulum ya ce duk wani dan gudun hijira dake da muradin komawa muhallinsa na asali to yana da wannan zaɓi, domin gwamnatinsa a shirye take ta dauki wannan ɗawainiya.
Ya kara da cewa wadanda tuni aka wanzar da zaman lafiya a yankunansu ka iya, kazalika su sauran kuma za a maida su zuwa wani wuri ba shi da sarkakiya don ci gaba da gudanar da rayuwarsu.
Comments 1