Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya kori mutane 25 daga cikin sakatarorin kananan hukumomi ashirin da bakwai da ke jihar.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwar dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar kananan hukumomin jihar Najib Umar ya fitar, Kuma ya rabawa manema labarai a jihar.
Sanarwar ta ce Gwamnan ya sauke dukkannin sakatarorin kananan Hukumomin jihar baki daya Amma banda na kananan hukumomin Sule Tankarkar da Buji.
Sai dai ya umarce su da su gaggauta mika dukkan kayan aikin ga shugabannin kananan hukumomin da ke kula da harkokin gudanarwa da ayyukan su (DAGS).
KARANTA WANNAN LABARIN: Sanata Uba Sani ya Caccaki Shehu Sani Kan Toshe Sashin Bayyana Ra’ayi a Facebook
Duk da cewa, sanarwar bata bayyana dalilan sallamar sakatarorin ba, Amma Gwamnan ya yaba da irin gudunmawar da kujerun Sakatarorin Kananan Hukumomin suka bayar tare da yi musu fatan samun nasara a harkokinsu na Nan gaba.