Hukumar kula da Ma’aikatan Jihar Jigawa ta ce, ta karawa Ma’aikatan Jihar guda 10,540 matsayin daga shekarar 2016 zuwa shekarar 2020.
Shugaban hukumar Alhaji Lawan Abdu Babura ne ya bayyana hakan, a lokacin da yake tattauna wa da manema labarai a garin Dutse, babban birnin jihar.
Inda ya ce, ma’aikata 1,827 an karamusu girma ne a shekarar 2017, sai 2,554 aka karamusu matsayi a shekarar 2018, ya yin da guda 2,304 kuma suka Sami Karin girman a shekarar 2019, da kuma ma’aikata 2,697 da su ma suka sami karin girma a shekarar 2020.
KARANTA WANNAN LABARIN: Chelsea ta dauki aron Soul, PSG ta ki Saida wa Madrid Mbappe
Allhaji Lawan ya kara da cewa, hukumar ta kuma karawa Ma’aikatan 1,661 matsayi, a cikin wannan shekarar ta 2021, ya yin da haryanzu hukumar ke kokarin yima wasu Ma’aikatan karin girma.
Kazalika ya ce a kalla ma’aikata 1,760 ne su ka yi ritaya daga aikin su, a tsakanin shekarar 2016 zuwa 2020.
A wani labarin Kuma na daban
Mukaddashin shugaban jam’iyar PDP na Kasa Yemi Akinwonmi a jiya Talata, ya jagoranci tawagar Shuwagabannin jam’iyar, domin ziyarar Tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan a gidan shi dake babban birnin tarayya Abuja.
Wadanda shuka raka Akinwonmi sun hada da tsohon sakataran ruko na jam:Iyar a yankin Kudu maso Yammacin kasar nan Daisi Akintan, da kuma daya daga cikin mambobin kwamitin zartarwar jam’iyar Mrs Helen Taiwo.
Dukkannin su uku, sun gana da Tsohon Shugaban kasa ne a sirirran ce, da ake kyautata zaton cewa, sun na bukatar Jonathan ne da ya ci gaba da zama a Jam’iyar PDP, tare da basu ingantacciyar shawara da za ta taimaka wajan magance rikice-rikicen da suka dabai-baye jam’iyar.
Wata majiya da ke da masaniya game da taron ta ce, “Tawagar jam’iyar na shiyar Kudu maso Yammacin kasar nan, sun gana da tsohon Shugaban kasar ne, don rokon sa, da kada ya fice daga jam’iyyar.”
“Sun Kuma bukace shi, da nuna damuwar shi da jam’iyar, ta hanyan shiga al’amuranta na yau da kullun, inda shi ma Tsohon Shugaban kasar, ya bai wa tawagar tabbacin cewa, bazai fice daga jam’iyar ba” a cewar majiyar.