Gwamnatin jihar Jigawa ta karbi Almajirai 524 ‘yan asalin jiharta daga hannun makwabciyarta wato gwamnatin jihar Kano.
A yayin da yake karbar Almajiran a sansanin NYSC na Janar Yakubu Gowon dake Dutse, Gwamna Muhammad Badaru ya ce za a yi wa almajiran gwajin lafiya daga bisani a mika su zuwa ga Iyayensu.
Badaru ya ce tuni suka shirya yadda za a killace su da ciyar da su har sai an tabbatar suna cikin koshin lafiya kafin a kai ga mika su zuwa ga Iyayensu. Ya ce za su yi hakan ne domin tabbatar da cewa Almajiran na cikin koshin lafiyar da za su iya shiga cikin al’umma.
Sunusi Kiru, Kwamishinan Ilimi na jihar Kano, wanda kuma ya jagoranci kwashe almajiran zuwa jihohinsu, ya tabbatar da cewa sai da aka yi musu gwaji kafin a kai ga tura su jihohinsu.
Gwamnatin jihar Kano na maida Almajirai jihohinsu a wani mataki na dakile yaduwar cutar Korona.
-Leadership A Yau