By Abbas Yakubu Yaura
Kasa da sa’o’i 24 da amincewa da majalisar dokokin jihar Jigawa tayi, a ranar Larabar data gabata ne gwamna Badaru Abubakar ya rattaba hannu kan kudurin kasafin kudin jihar na Naira biliyan 177.7 na shekarar 2022, tare da yin alkawarin tabbatar da aiwatar da shi.
A ranar Talata ne majalisar dokokin jihar ta amince da kasafin kudin shekarar 2022 na naira biliyan 177.7bn da gwamnan ya gabatar mata a ranar 10 ga watan Nuwamba, wanda ya kunshi Naira biliyan 53bn na kudin ma’aikata, da naira biliyan 90.8bn na shirin bunkasa jari, da sauran kudaden da ake kashewa da suka kai Naira biliyan 33.9bn.
Shugaban kwamitin kasafin kudi kuma mataimakin kakakin majalisar, Suleiman Musa Kadira, ya mika rahoton kwamitin nasa tare da shawarwarinsa, wanda majalisar ta amince dashi baki daya.
Gwamnan ya bayyana godiyarsa ga bangaren majalisar dokoki bisa goyon baya da hadin kai da suke baiwa bangaren zartaswa domin ganin an gaggauta amincewa da kudirin, yana mai cewa za a fara aiwatar da wannan doka cikin gaggawa.