Gwamnatin jihar Kebbi ta bai wa hukumar Hisba naira milliyan dari, domin cigaba da gudanar da ayyukanta na wanzar da zaman lafiya a fadin jihar nan.
Gwamna Abubakar Bagudu ne ya bayyana hakan, a jiya lahadi wajen bikin cika shekara 20 da kafa hukumar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan sanda Sun Bindige Wani Da Ake Zargun Mai Garkuwa Da Mutane Ne
Bikin dai ya gudana ne a babban dakin taro na masaukin Shugaban kasa, dake nan birnin kebbi.
Gwamnan ya Kara da cewa gwamnatin jihar tabada kyautar kudaden ne amadadin majalisar dokokin jihar da ma shugabannin kannanan hukumomi 21 dake fadin jihar Kebbi.
Kazalika babban lauyan gwamnatin tarayya Kuma Ministan shari’a, Abubakar Malami SAN Wanda shi ne babban bako a wajen bikin ya bayyana bayar da kyautar naira biliyan biyar zuwa ga hukumar ta Hisba, inda shi Kuma dan takarar gwamnan jihar kebbi karkashin inuwar jam’iyyar APC Dr. Nasiru Idris Kauran Gwandu ya bayar da naira dubu dari biyar va Hukumar.
A WANI LABARI KUMA: An Ceto Mutane Tara A Yayin Da Ruwa Ya Rushe Gini A Legas
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta NEMA ta ce an ceto mutane 9 daga wani gini da ya rushe a yankin Maryland da ke Legas a ranar Litinin din nan.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Ko’odinetan yankin Legas na hukumar Ibrahim Farinloye ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya baiwa a gidan talabijin na Channels.