By Abbas Yakubu Yaura
Gwamna Abubakar Atiku Bagudu na jihar Kebbi, a ranar Alhamis, ya kaddamar da wani sabon katafaren ofishin hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC), wanda gwamnatin tarayya ta fara ginawa, kuma gwamnatin jihar Kebbi ta kammala aikin ginashi.
Bagudu, ya bayyana taron a matsayin mai matukar muhimmanci ga hukumar FRSC ta jihar Kebbi dama kasa baki daya.
Sannan yace “Yana da mahimmanci saboda yana taimakawa wajen samar da kayan aiki mai ƙarfafawa ga jami’ai da ma’aikatan ƙungiyar. A ci gaba da takaita albarkatu, FRSC wacce hukuma ce mai matukar muhimmanci ba a bata kulawa fiye da yadda ake ba wasu.
“Don haka dole in yaba wa shugaban hukumar da Corps Marshal bisa yadda suka yi amfani da filayen da gwamnatin jihar ta basu tare da kafa wannan tsari daya dace.”
Gwamnan jihar Kebbi ya kara yabawa kokarin da jami’an tsaron suka yi wajen samar da kayayyakin aiki iri daya a fadin Najeriya, tare da taimaka wa hanyoyin kasar su kasance masu aminci da tsaro.
“Jihar Kebbi ta kasance a koda yaushe yayin da al’ummomi daban-daban ke yabawa tare da nuna farin ciki da aiki tukuru da jajircewar jami’an tsaro.
“Za mu ci gaba da bada goyon baya da hadin gwiwa ga FRSC, hukumomin tsaro da sauran MDAs, don tabbatar da jin dadin jama’ar jihar,” in ji Bagudu.
“Mun kuduri aniyar rage kashe-kashe da ake yi a kan manyan titunan kasar, kuma ba za mu yi kasa a gwiwa ba ta wannan hanyar.”
Shugaban FRSC Dokta Boboye Oyeyemi, ya kuma yabawa Gwamna Bagudu bisa gagarumin gudummawar filin domin gudanar da aikin, tare da bada cikakken kayan aiki a garesu.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa aikin shi ne na 16 da aka kaddamar a cikin shekaru bakwai da suka gabata, inda yace zai samar da yanayi mai kyau ga jami’ai da maza a fadin Najeriya.
Boboye ya kuma bayyana cewa zai tura wata sabuwar motar sintiri zuwa ofishin a mako mai zuwa baya ga wata motar da gwamna Bagudu yayi alkawari basu.