By Abbas Yakubu Yaura
Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya yi kira da a dauki mataki kan kalubalen tsaro dake addabar yankin Arewa.
Gwamnan wanda ya yada a shafukan sada zumunta ya bukaci gwamnati data tashi daga halin ko-ta-kwana, inda ya nuna cewa tsaro a Arewa lamari ne na gaggawa.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin daya koka kan yadda kashe-kashen da ‘yan Fashi suka yi a jihohin Katsina da Sakkwato a baya-bayan nan yayin da yake jajantawa iyalan wadanda aka kashe.
Sannan yace, “Lokaci ya yi da za mu dauki kalubalen tabarbarewa tsaro a Arewa da muhimmanci.
“Ayyukan ‘yan fashi da kashe-kashe da suka kara ta’azzara a jihohin Katsina da Sokoto sun tunatar da mu cewa tsaro a Arewa lamari ne na gaggawa, kuma dole ne gwamnati ta tashi daga halin ha’ula’i zuwa daukar mataki.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa gwamnan yace “A madadin gwamnati da al’ummar jihar Bauchi, ina mika ta’aziyyata ga iyalan da suka rasa ‘yan uwansu a irin wannan mugun yanayi.”Allah ya gafartawa mamatan kurakuransu, kuma ya basu hutu.”