Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi a ranar Juma’a ya sanya hannu kan wata yarjejeniya da kamfanin PowerDot, wani kamfanin samar da hasken lantarki dake Birtaniya domin samar da wutar lantarki ba tare da yankewa ba cikin sauki.
Gwamnan ya sanya hannu bisa yarjejeniyar da suka kulla na Dala miliyan saba’in, domin samar da megawatts goma na wutar. A yayin sanya hannun gwamnan na tare da wadansu mukarrabansa.
Da yake magana bayan sanya hannu, Gwamna Bala ya yi alkawarin bada hadin kai da gudummawa wajen ganin an cimma yarjejeniyar da aka kulla.