Gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello, ya jaddada kudirinsa na magance kalubalen rashin tsaro a jihar.
Gwamnan wanda ya yi nuni da cewa ya ki amincewa da biyan kudin fansa inda kuma ya ce gwamnatin sa na kan bin diddigin wadanda suka yi garkuwa da mahaifiyar shugaban ma’aikatan sa (CoS), Misis Seriya Raji.
Gwamna Bello ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a Lokoja, wajen wani taron addu’o’i na musamman da kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) ta shirya bisa bin umarnin Mai Martaba Sarkin Musulmi Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar lll, Kuma Shugaban JNI na yi addu’ar zaman lafiya a kasar nan.
Gwamna Bello wanda ya samu wakilcin Alhaji Salihu Sani, SSA mai kula da harkokin addini (SSA) ya yabawa shugaban JNI bisa wannan shiri, yana mai cewa dole ne kowa ya tashi tsaye domin ganin an kawo karshen ‘yan fashin da suka addabi kasar nan.
Kazalika ya Kuma jaddada cewa, tare da hadin gwiwar kowa da kowa, za a magance matsalar garkuwa da mutane da sauran laifukan da suka jibanci aika laifika, kuma al’umma za su ci gajiyar zaman lafiya da ake bukata.
A nasa jawabin, Ambasada Usman Bello, shugaban JNI na jihar Kogi, ya ce an gudanar da addu’o’in na musamman ne don a taimaka wa shugabanni su samu hikimar daukar kwararan matakai domin samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasa baki daya.