Daga: Comrd. Haruna Sardauna
Gwamna Mai Mala Buni yana daya daga cikin gwamnoni uku da sukayi rakiya ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, zuwa Kasar Liberia, domin halartar Bukin cikar kasar shekara 172 da Samun Yancin Kai.
Shugaba Muhammadu Buhari, ya kasance Babban Bako na Musamman a filin Bukin tunawa da ranar samun Yancin Kai, gwamnatin Kasar Liberia ta karrama shi da lambar girmamawa, a yau Juma’a.
A kullum gwamna Mai Mala Buni, yana sake kusanci ga shugaba Muhammadu Buhari, saboda kwazo da halayyar su, tana kamanceceniya, kyakkyawar alakar dake tsakanin su, abin alfahari ne ga al’ummar jihar Yobe.