Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya yi alhinin rasuwar mutane uku da wasu shida da suka samu raunuka da dama a wani hatsarin mota da ya afku a hanyar Potiskum zuwa Bauchi.
Gwamna Buni a wata sanarwa da mai magana da yawun sa, Mamman Mohammed ya fitar a ranar Lahadin da ta gabata ya bayyana hatsarin a matsayin abin ban tsoro.
KARANTA WANNAN LABARIN: Jam’iyyar APC Ta Kaddamar Da Daraktoci 22 Na Yakin Neman Zaben Gwamna
“Mutuwar da aka samu da raunukan sun kasance masu matukar tayar da hankali, amma wannan lokaci ne da aka ayyana da yardar Allah,” in ji shi.
Buni ya yi addu’ar Allah ya gafarta musu kurakurensu, ya jikan su da Aljannar Firdausi, da iyalansu, ya kuma baiwa iyalansu hakurin jure wannan rashin mai radadi.
Ya kuma yi addu’ar Allah ya baiwa wadanda suka samu raunuka daban-daban da ke barazana ga rayuwarsu sauki cikin gaggawa.
Kazalika, Gwamna Buni ya jajantawa wadanda bala’in gobara ya rutsa da su a unguwar Sabon Pegi a cikin birnin Damaturu.
Gwamna Buni ya bayyana lamarin da ya shafi wasu shaguna a matsayin abin bakin ciki da takaici.
A wani labarin kuma, Ciwon Daji Yana Hallaka ‘Yan Afirka 700,000 a Kowace Shekara – WHO
Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce kusan sabbin masu kamuwa da cutar kansa miliyan 1.1 na faruwa kowace shekara a Afirka, inda kusan 700,000 ke mutuwa.
Daraktar WHO a Afirka, Dr Matshidiso Moeti, ta bayyana hakan a ranar Lahadi a cikin sanarwarta na bikin ranar cutar daji ta duniya na bana mai taken ‘Rufe Tazarar Kulawa: Haɗa Muryoyinmu da Daukar Mataki’.