By Abbas Yakubu Yaura
Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya bayyana kaduwarsa bisa rasuwar dan mataimakinsa, wanda ya rasu a wani hadarin mota da ya rutsa da su da wasu mutane biyu.
Gwamnan ya jajantawa mataimakin gwamnan, Idi Barde Gubana, wanda ‘yan uwa suka yi hatsarin mota a kan babbar hanyar Maiduguri zuwa Kano.
- KARANTA WANNAN LABARIN: 2023: Atiku Abubakar Ya Magantu Kan Zabar Abokin Takarar Sa
Gwamnan ya yi addu’ar Allah ya baiwa wadanda suka samu raunuka a hadarin sauki cikin gaggawa.
Hakazalika, Buni ya jajantawa Maina Digma Gana, dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Fune, bisa rasuwar diyarsa, da kuma iyalan marigayi Alh.Ado Garba.
Gwamna Buni ya bayyana mutuwar a matsayin abin bakin ciki da ban tsoro “amma wannan shi ne nufin Allah (SWT), mahaliccinmu.
“Lokaci ya yi da za su tashi daga Duniya kuma muna rokon Allah (SWT) Ya gafarta musu kurakuran su, ya kuma sa su huta a Aljannatu Firdausi.
“Allah kuma ya baiwa iyalansu karfin halin jure babban rashi” gwamnan yayi addu’a.
Comments 1