Dakta Mohammad Idris, kwamishinan ilimin bai daya na jihar Yobe, a ranar Talata ya ce nan ba da dadewa ba jihar za ta kafa karin makarantun sakandare na mata guda biyar.
Idris, wanda ya bayyana haka a Damaturu lokacin da wasu kungiyoyin mata uku suka kai masa ziyarar ban girma, ya ce makarantun za su inganta ilimin fannin yara mata.
Kungiyoyin sun hada da (SGBV), Kungiyar Mata Musulmi ta Najeriya (FOMWAN) da kuma Kungiyar Mata Kiristoci ta Najeriya (WOWICAN).
A wani labarin Kuma na daban.
Iyayen daliban makarantun firamare na karamar hukumar (LEA) dake babban birnin tarayya Abuja sun nuna damuwarsu kan yajin aikin da malamai ke ci gaba da yi a fadin yankin don haka suka yi kira ga karamar ministar babban birnin tarayya, Hajiya Ramatu Tijjani Aliyu da ta shiga tsakani.
Iyayen dai sun ce yajin aikin yana da matukar barazana a gare su, tare da bayyana cewar akwai yiwuwar ‘ya’yansu su shiga wani mawuyacin halin.
Daya daga cikin iyaye mai suna Misis Zainab Alhassan ta ce, “Ina da ‘ya’ya uku a makaranta, kuma tun da aka fara yajin aikin, kullum suna fita wasan kwallon kafa ne, sai da na dauko musu wani malami Kuma duk da haka, nan da nan bayan darasin, sai su bace su je su buga kwallon kafa, abin da ban ji dadinsa ba.”
Don haka ta yi kira ga hukumar FCTA da masu ruwa da tsaki a harkar ilimi da su sa baki domin ganin yadda malamai da shugabannin kansilolin za su hau kan teburin tattaunawa.
Wani daga cikin iyaye Mohammed Kabiru, ya ce abin takaici ne yadda shugabannin majalisar suka gaza cika yarjejeniyar da suka kulla da malaman duk da tsoma bakin Sanata Philip Aduda da FCTA a baya.
Ya ce abin takaici ne yadda yara ke ci gaba da zama a gida har na tsawon makonni ba tare da nuna wata damuwa ba da shugabannin majalisar wajen tattaunawa da malaman.
Kazalika ya ci gaba da cewa, “A gaskiya tun bayan wannan yajin aikin, ‘ya’yana biyu suna gida, kuma idan ba a dauki matakin gaggawa ba, hakan na iya shafar makomar yaran, domin ba kowadanne iyaye ne ke da kudin da zai tura yaronsa zuwa makarantun kudi masu zaman kansu ba.”
Shima wani uba Mista Kehinde Afolabi, ya ce abin kunya ne yadda Abuja, wadda ita ce zuciyar al’ummar kasa, za ta bari ilimin yara ya ci gaba da fuskantar koma baya a hannun masu ruwa da tsaki.
Mista Afolabi ya ce, “Idan da gaske sun damu da fannin ilimi, da sun ba da fifiko ga jin dadin malamai. Amma ku dubi yadda suke kashe kudaden yakin neman zabe yayin da yaranmu ke ci gaba da zama a gida.”