Gwamnan jihar Bayelsa Douye Diri zai ɗaukaka ƙara bayan da wata kotun sauraran ƙararrakin zaɓe dake zamanta a babban birnin tarayya Abuja ta soke zaɓensa.
A dai kwanakin baya ne tsohon gwamnan jihar Seriake Dickson ya nemi kotun ƙoli ta sake yin nazari kan hukuncin da ta yanke kan zaɓen gwamnan na jihar ta Bayelsa.
A jiya ne dai wata kotu dake zamanta a birinin tarayya Abuja ta soke zaɓen gwamnan jihar Bayelsa Douye Diri, inda ta bada umarnin fara shirye –shirye domin gudanar da wani sabon zabe a jihar.
https://dimokuradiyya.com.ng/dalilan-da-ya-sanya-kotu-ta-soke-zaben-gwamna-diri-na-jihar-bayelsa/
Mai shari’a Muhammad Sirajo ne ya jagoranci alƙalai guda uku wajen soke zaɓen, inda ya ce an gudanar da zaɓen ba bisa ƙa’ida ba, duba da cewa an cire jam’iyyar PDP da ɗan takarar ta King George tun a ranar 16 ga watan Nuwanban 2019
Tun da farin dai jam’iyyar hamayya ta PDP ce ta shigar da ƙarar gaban kotu tana ƙalubalantar hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa kan kin basu dama a zaɓen.
Tuni dai kotun ta bai wa hukumar zaɓe INEC umarnin sake gudanar da wani zaɓen gwamnan a jihar cikin kwanaki 90 masu zuwa.