By Abbas Yakubu Yaura
Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, a ranar Laraba ya ce akalla mutane 387 aka rasa a kananan hukumomin Kauru da Zango Kataf na jihar cikin shekaru biyu.
Wannan dai na zuwa ne a dai dai lokacin da gwamnan ya koka kan sabon kashe-kashen da aka yi a kananan hukumomin biyu, inda wani manomi ya sare kan wani Bafulatani makiyayi a ranar Litinin.
El-Rufai ya nanata kiran da ya yi tun farko ga al’ummomin kananan hukumomin biyu da su kasance masu bin doka da oda a kodayaushe, kuma su guji yin garambawul, wanda hakan zai ci gaba da dagula harkokin tsaro.
Gwamnan wanda ya samu wakilcin kwamishinan tsaro na cikin gida Samuel Aruwan ne ya bayyana haka a wani taron gaggawa na tsaro da ya kunshi sarakunan gargajiya da malaman addini da na al’umma daga kansiloli a fadar Agwatyap A̠tak Njei a karamar hukumar Zangon Kataf a yanki.
Ya bayyana cewa, a cikin shekaru biyu an yi asarar rayuka 387 a rikicin tsakanin kabilun Atyap, Fulani, Chawai, Irigwe da Hausawa a kananan hukumomin Kauru da Zangon Kataf.
Kwamishinan ya samu rakiyar shugabannin hukumomin tsaro a wajen taron.
Ya ce, “Muna nan a madadin gwamna sakamakon sake kashe-kashen da aka yi a kananan hukumomin Kauru da Zangon Kataf. Babban koma baya ne amma ba za mu ja da baya ba.
“Muna sake jaddada rokonmu na neman bin doka da kuma kaucewa yin fadan baki daya. Wadannan kashe-kashe da lissafin kashe-kashen ba gaskiya ba ne.
“Misali a shekarar 2020, an kashe ‘yan kasa 114 a Zangon Kataf da 28 a Kauru, sannan a shekarar 2021, an kashe 186 a Zangon Kataf da 59 a Kauru; idan ka hada alkalumman, mun rasa mutane 387 a wadannan kananan hukumomin biyu. A cikin shekaarar 2021, ‘yan ƙasa 100 sun ji rauni da harbin bindiga a dai wadannan kananan hukumomin biyu – 77 a Zangon Kataf da 23 a Kauru.
“Wannan baya ga kona gidaje da matsugunan da aka kona, an lalata gonaki, an kashe shanu da kuma durkushewar tattalin arzikin karkara da ya shafi daukacin al’umma.
“Dole ne mu tashi tsaye don dakatar da duk waɗannan ƙalubalen da ke tasowa daga halayen wasu abubuwa na kowane bangare. Mu yi tunani tare, mu kawar da wannan zubar da jini mara dalili.”
Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Zangon Kataf/Jaba Amos Magaji, ya goyi bayan wannan kira na neman bin doka da kamfen tare da zaman lafiya a wuraren.