Gwamna El-Rufa’i na jihar Kaduna ya sasauta dokar hana fita na awa 24 a ƙananan Hukumomin Jema’a da Kaura da yankin kudancin jihar da aka sanya a makonni biyu da suka wuce sakamakon hare-haren da aka kai a yankin Masarautar Zikpak.
Dokar da aka sassauta daga 6.00 na safe zuwa 6.00 na yamma kuma ta fara aiki a ranar alhamis, bayan sanarwar da kwamishinan tsaro da harkokin cikin Gida Samuel Aruwan ya fitar.
Ya ce ɗaukar matakin ya biyo bayan rahoton jami’an tsaro bayan sun bibiyi lamarin kuma suka bayar da shawarar rage dokar.
“A dalilin haka ne muka sassauta dokar da za ta koma daga ƙarfe shida na safe zuwa karfe shida na yamma a kullum”, inji sanarwar.
Sai dai sassaucin bai shafi ƙananan hukumomin Kauru da Zangon Kataf ba, inda ya ce ana ci gaba da duba yiwuwar hakan nan gaba bayan lura da yadda hali yayi.
An sanya dokar hana fita na awa 24 ne a ƙananan hukumomin Jema’a da Kaura bayan kai harin ranar Jumma’a, 24 ga watan Yuli a wasu yankuna na ƙananan hukumomin biyu.
A ƙananan hukumomin Kauru da Zangon Kataf, inda sabon rikicin kudancin Kaduna ya farfado, an sanya dokar hana fita ne a ranar 11 ga watan Yuni, inda suke tunkarar makonni goma a cikin dokar.
Sai dai mazauna yankin da dama sun koka dangane da dokar duba da irin halin matsi an rayuwa da ake fuskanta a halin yanzu.
“Gaskiya mun ji dadin sassauta wannan dokar, babu abun da ya kai zaman lafiya dadi”, Inji wasu da Aminiya ta zanta da su.