Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri ya bayar da gudunmuwar Naira miliyan 27 ga iyalan Birgediya Janar Dzarma Kennedy Zirkushu da sojoji uku da mayakan Boko Haram suka kashe a garin Chibok na jihar Borno kwana-kwanan nan.
Janar Zirkushu, Kwamandan Rundunar hadakar jami’an tsaro ta Task Force na 28 dake garin Chibok, Manjo da wasu sojoji biyu sun mutu ne a wani harin kwantan bauna da aka yi musu a hanyarsu ta zuwa bayar da tallafi ga wani sansanin soji da ke Askira Uba a wani hari da kungiyar ISWAP ta kai.
Gwamna Fintiri ya ce tutar kasar za ta kasance a kasa na tsawon kwanaki uku yayin da za’a sauya wa shahararren titin Legas da ke Yola suna don karrama Janar Zirkushu.
Ya ce, “A matsayin tallafi, ina baiwa iyalan Birgediya Janar Zirkushu kudi N10m, da kuma wani N17m ga iyalan sauran sojoji uku da suka mutu tare da shi.”
Idan za’a iya tunawa dai, An yi jana’izar Janar Zirkushu da wasu sojoji a ranar Juma’a a makabartar sojoji da ke Barikin Gibson dake garin Jalo a Yola na jihar Adamawa ne a jiya Asabar