Gwamna Fintiri na jihar Adamawa ya sake bada umurnin garkame jihar na wadansu makonni biyu wanda dokar za ta fara aiki daga daren Juma’ar 24 ga watan Afrilu.
Daraktan watsa labarai na gwamna Ahmadu Fintiri, Solomon Kumamgar, shi ne ya fitar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a a Yola.
Fintiri ya ce dokar garkame jihar zai kare ne a ranar 8 ga watan Mayu. Gwamnatin jihar ta ce ba ta da wani mataki da za ta iya dauka da ya wuce wannan a matakin dakile Korona.