Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri ya sanya hannu a kudurin dokoki uku inda suka zama doka kamar yadda Attoni Janar na jihar kuma Kwamishinan shari’a, Afraimu Jingi ya tabbatar a Birnin Yola a ranar Litinin.
Dokokin uku sun hada da; samar da Hukumar tsaftar muhalli ta jihar (ADSEPA), da kuma samar da Hukumar kare cin zarafin al’umma ta jihar (VAPP) da kuma dokokin ka’ida ta jihar Adamawa inda ita ma ta zama doka.
Jingi ya shaidawa manema labarai cewa dokar ADSEPA an samar da ita ne domin ta kare muhalli daga fuskantar zaizaya a kowanne lokaci.
Ya shaida cewa dokar tana da bangarori biyar dauke da sashe 37 wanda ya hada da bayani, alfanu, kasafin kudi, walwala, laifuka, hurumi da kuma karfin hukumar.
Kwamishinan har wala yau ya ce dokar VAPP za ta hana dukkanin wani nau’in cin zarafin al’umma tare da bada kariya da kuma sauki ga wadanda abin ya shafa da kuma hukunta wadanda aka kama da aikata laifin.