By Abbas Yakubu Yaura
Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Fintiri ya sabunta dokar hana fita da aka kafa a kananan hukumomi uku na Yola ta Arewa da Yola ta Kudu da kuma Girei.
DUBA WANNAN LABARIN: Sakataren APGA na kasa, Labaran Maku ya koma PDP
An kafa dokar hana fitar dare tun da farko biyo bayan ayyukan ‘yan daba da sauran miyagu masu amfani da baburan Adaidaita sahun da motoci.
“An kafa dokar hana fita, wanda ta kasance daga karfe 10:00 na dare. zuwa 5:00 na safe, yanzu an sauƙaƙa lokacin farawar dokar daga karfe 11:00 na dare zuwa karfe 5:00 na safe a kullum bayo bayan shigowar azumin Ramadan. Sabuntawar ta fara aiki nan take,” a cewar wata sanarwa daga fadar gwamnati.
Sanarwar da Sakataren Yada Labarai na Gwamna Fintiri Mista Humwashi Wonosikou ya fitar a Yola a jiya ta ce: “An samu cigaban sabunta dokar ne don ba wa Musulmi masu aminci damar yin tafsiri a lokacin.”
A watan Fabrairun shekarar 2021 ne gwamnatin jihar ta sanya dokar hana zirga-zirgar dare a kananan hukumomin uku ta hanyar dokar hana zirga-zirgar babura a jihar Adamawa mai lamba 1 na shekarar 2021.
Umurnin, wanda ke nufin duba wuce gona da iri na ’yan fashin da ke addabar yankunan, ya sanya hukuncin zaman gidan yari na watanni shida tare da zabin biyan tara ko duka biyun gawanda yayi watsi da umarnin hana hawa babur mai kafa uku ko mota.
Sakamakon sake duba dokar ta-bacin da aka yi a halin yanzu, Gwamna Fintiri ya umurci hukumomin tsaro da su kara kaimi wajen tabbatar da tsaro a fadin jihar, musamman a karamar hukumar Yola ta Arewa da karamar hukumar Yola ta Kudu da kuma Girei ta hanyar tura karin jami’an tsaro da za su ci gaba da sanya ido, in ji sanarwar ta Gidan gwamnati .