Gwamna Abdullahi Umar Ganduje Gwamna ne mai kawo sauyi. Babu jayayya game da wannan batu. Shin kun taba tunanin dalilin da yasa kwanan nan gwamnan ke dada samun lambobin yabo na kyakkyawan jagoranci da kuma siyasa?
Ya kasan ce ya na gudanar da al’amuran shi jihar ta Kano da kwarewa Mai ban ban mamaki. Kazalika a bangaren shugabanci da siyasa ba shi da na biyu.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ambaliyar ruwa ya kashe Mutum 52 a Jamhoriyar Niger
Fiye da shekaru shida, ya na gudanar da kula da mulkinshi tare da kabilu daban -daban a jihar Kano, cikin kauna da kishin ƙasa.
A fannin jagorancin shi tsaro ne na a matakin farko. Idan ba haka ba me ya sa kuke ganin gwamnan kwanan nan ya ƙaddamar da Shirin ‘Yan Sanda na Al’umma, don Masarautar Rano, inda dajin Falgore ya ke?
Bugu da kari, idan kuka tattara manyan ayyukan da Baba Ganduje ya bayar da kuma zaman lafiyar da jihar ta more, tabbas za ku fahimci cewa, jihar Kano ta na kan madai-dai-ciya na zama ɗaya daga cikin manyan biranen duniya, wanda shine fifikon gwamna da wasu na daban.