Babban Sakataren Kungiyar Kasashe Masu Fitar da Man Fetur (OPEC), Muhammad Sunusi Barkindo, ya bayyana gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano a matsayin mai kaskantar da kai kuma mai mayar da hankali, wanda ke yin aiki sosai duk da kalubalen da ake fuskanta.
ya bayyana hakan ne, ya yin wata ziyarar ban girma da ya kaiwa gwamnan, a Gidan Gwamnatin Kano, a jiya Alhamis, tare da wasu iyalan shi,, da abokannan sa.
Barkindo ya Kuma bayyana cewa, “Ya yi aiki sosai duk da ƙalubalen da ke tattare da shugabanci. Ka ci gaba da zama gwamnan jama’a ” inji shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: EFCC ta kama tsohon gwamnan Abia da Dan shi
“Kana mai da hankali sosai kan aikin ka, mai tawali’u. Na tabbata Allah ya kawo ka da wata manufa. Ya yin da ka ke sauke nauyin da ya rata ya a wuyanka,” a cewar shi.
Ya ci gaba da cewa, “Za mu ci gaba da tallafa ma gwamnatin jihar Kano, donmin bunkasa ci gaba jihar baki daya.”
Ana sa jawabin, gwamna Ganduje ya aminta da ingantaccen jagoranci, Barkindo ke bayarwa OPEC, yana mai jaddada cewa, “Dole ne in taya ku murna kan yadda kuka yin aiki a OPEC”
“Kano ta yi farin ciki da kyakkyawan aikin da kuke yi a matakin na duniya. Muna kuma farin cikin dangane da girmamawar da kuke yi wa jihar Kano,” in ji shi.
Comments 1