By Abbas Yakubu Yaura
Olubadan na yankin Ibadan, Oba Lekan Balogun, ya bayyana shirinsa na karfafa alakar da ke tsakanin jihar Oyo da Arewa domin tabbatar da cewa kasar nan ta kasance lafiya ga kowa ba tare da la’akari da kabilar harshe ko addini ba.
Olubadan ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya karbi bakuncin Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Ganduje, da Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, a ziyarar da suka kai wa sabon sarkin da aka nada a Ibadan ranar Asabar.
Oba Balogun dai ya samo asali ne tun shekaru da dama da suka shige tsakaninsa da jihar Kano, tun daga abokantakarsa da Marigayi Abubakar Rimi da Balarabe Musa, wadanda dukkansu tsaffin gwamnonin jihohin Kano da Kaduna ne.
DUBA WANNAN LABARIN:‘Yar Majalisar Gombe Ta Baiwa Mata 300 Tallafin Kudi Naira 10,000
Sarkin ya tunatar da cewa a matsayinsa na tsohon malami a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, kuma darakta a Jaridun Triumph mallakin Jihar Kano, ziyarar Ganduje ta sake farfado da tunanin zamanin da aka yi a Arewacin kasar nan.
Ganduje ya tunatar da Olubadan cewa Ibadan gida ne ga kowane dan jihar Kano, inda ya kara da cewa bayan auren ‘yarsa da Idris Ajimobi, dan gidan tsohon gwamnan jihar Oyo, Sanata Abiola Ajimobi, ta hanyar zamantakewar aure ya zama wani bangare na birnin, “Duk abin da ya shafi Ibadan ya shafe ni.”
Gwamnan, a cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaran sa, Abba Anwar, ya fitar, ya tunatar da cewa sanin dangantakar da ke tsakanin sabon Olubadan da marigayi Rimi ya kara karfafa soyayyar sa ga sarkin, wanda ya umurce shi da ya ci gaba da kokari wajen ganin an samu ci gaba da hadin kan masarautar.
Sarkin kano Aminu Ado Bayero ya shaida wa Olubadan cewa gwamnati da kuma cibiyoyin gargajiya na jihar Kano suna murna da shi a matsayin daya daga cikinsu, inda ya bukace shi da ya dore da dadewa da dankon zumuncin da ke tsakanin masarautun biyu.
Fitattu daga cikin manyan baki da suka raka tawagar Kano zuwa fadar Olubadan akwai tsohon sakataren gwamnatin jihar Oyo, Olalekan Alli; tsohon mai ba da shawara na musamman ga Ajimobi, Bolaji Tunji; da Idris Ajimobi, wanda ya kasance surukin gwamna Ganduje ne.