Gwamna Ganduje Ya Kaddamar Da Kwamitin Gudanarwar OGP A Kano
Don ci gaba da karfafa kokarin tabbatar da kyakkyawan shugabanci da bunkasa jihar Kano, gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya kaddamar da kwamitin gudanarwa na haɗin gwiwar kungiyoyi masu zaman kansu da Gwamnati a Shirin (OGP), yayin taron majalisar zartarwar jihar, a jiya, Laraba, a Africa House, dake Kano.
Jagorancin kwamitin ya kunshi mutane tara daga bangaren gwamnati, wasu mutane tara daga kungiyoyin fararen hula da kuma wasu mashawarta biyu daga bangaren gwamnati. Sakataren dindindin na Majalisar da Abdulrazaq Alkali daga Kungiyar Hadin Kan Al’umma (OCCEN) su ne Shugabannin wannan Kwamitin.
Tare da sanya hannu kan Dokar Zartarwa ta OGP, a lokacin mulkin Gwamna Ganduje na farko, Hukumar Korafi da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar, karkashin Barista Muhuyi Magaji Rimingado, ke dauke da Sakatariyar OGP ɗungurungun a jihar.
Rimingado ba tare da gajiyawa ba a fagen yaki da cin hanci da rashawa, ya samar da dama ga kasancewar jihar ɗaya daga cikin al’ummomin da ba su da cin hanci da rashawa. Ci gaban da gwamna ya yarda dashi sau ba adadi. wanda hakan na Daga cikin manyan dalilai kuma shine yasa Kano tayi fice a ɓangaren ayyukan OGP a cikin ƙasar nan.
A lokacin kaddamarwar, gwamnan ya bada tabbacin cigaba da marawa duk manufofin kungiyar ta OGP baya, yana mai yaba wa da yadda kawancen ya taimaka wajan nuna gaskiya da rikon amana a jihar sa a farkon mulkin sa na 2015.
“A koda yaushe muna yin imanin cewa, Dole ne a tallafawa Abokantaka da Gwamnati. Saboda hakan sadaukarwa ne ga Al’umma, Inji shi.