Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya kaddamar da yakin neman zaben dan takarar gwamnan Kano Dakta Nasiru Yusuf Gawuna, da mataimakinsa Murtala Sule Garo.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa Taron kaddamar da takarar ta su ya gudana ne a yamacin yau laraba a garin Gaya.
KU KARANTA: NAWOJ Ta Bukaci Mata Yan Jarida Su Karkata Kan Rahotannin Matsalolin Jinsi
Gwamnan jihar kano Abdulahi Umar Ganduje ne ya jagoranci kaddamawar, inda gwamnan ya bayyana cewa mataimakin sa wanda kuma shine dan takarar gwamna Nasiru Yusuf Gawuna da kuma tsohon kwamishinan kananan hukumomi Murtala Sule Garo a matsayin wadanda suka cancanta a saka a gaba a matsayin shugabannin da zasu cigaba da wanzar da ayyukan cigaba a jihar Kano.
A cewar Gwamnan hakan Ya zama dole sakamakon abinda ya kira gogewar aiki da gwagwarmayar siyasa da kowannen su ya samu tun daga matakin karamar hukuma wanda hakan ya sanya suka fahimci abinda al’umma ke bukata don bunkasar rayuwar su.
Da yake jawabi yayin taron dan takarar gwamnan Nasiru Yusuf Gawuna ya bayyana gwamna Ganduje a matsayin mai dattaku, hangen nesa da son ci gaban kanawa la’akari da yadda ya kawo ayyukan gina kasa da cigaban jama’a musammán matasa, inda yace yayi mamakin yadda suka sukayi dandazo domin ganin yadda jam’iyyar APC zata kaddamar yakin neman zaben ta a garin Gaya.
Dr Gawuna, ya kuma ce suna kara mika wuya ga Allah domin shine wanda ke bada mulki ga wanda yaso.
A nasa bangaren shugaban jam’iyyar APC na jihar kano Abdullahi Abbas yace zasu iyakacin iyawar su don ganin jam’iyyar ta samu nasara tun daga kasa har sama.
Taron na yau dai ya kasance rana ta farko da shugabanni da ‘yan takarkaru a matakai daban daban suka tsunduma neman ra’ayin al’umma, don samun nasara a kakar zaben badi dake karatowa wanda a Larabar nan gwamnan kano Abdullahi Umar Ganduje ya jagoranci tawagar masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a matakin jiha, don fara zagayen kananan hukumomin jihar nan 44 da nufin tuntuba da kuma neman goyon bayan jama’a.
Gangamin na yau ya samu halartar manya da kananan ‘yan jam’iyya da suka hada da shugaban Daraktan yakin neman zaben Gawuna da Garo Injiniya Rabi’u Sulaiman Bichi, shugaban jam’iyyar APC Abdullahi Abbas da sauran su.
A wani labarin kuma: 2023: Atiku zai gana da Gwamnonin G-5 – Okowa
Gwamnan jihar Delta kuma dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Ifeanyi Okowa, ya bayyana cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Atiku Abubakar, zai gana da gwamnonin G-5, domin kawo karshen matsalolin da suka dabaibaye jam’iyyar.
Sanata Okowa ya kuma karyata ikirarin cewa jam’iyyar ta yanke shawarar yin watsi da Gwamnonin Integrity G-5 da Gwamna Nyesome Wike ke jagoranta tare da yin gaba da zaben shugaban kasa a 2023.
Okowa, wanda ya bayyana hakan a ranar Laraba a Yenagoa bayan taron kungiyar gwamnonin Kudu-maso-Kudu tare da Gwamna Udom Emmanuel na Akwa Ibom, Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo da kuma mai masaukin baki, Sanata Douye Diri, ya ce PDP za ta warware matsalar dukkan batutuwan nan ba da jimawa ba, kuma ba za su bari Gwamnonin G-5 su fice daga jam’iyyar ba.