Gwamnatin jihar Kano ta daga dajarar asibitin garin Rano zuwa asibitin kwararru mai dauke da gadaje dari hudu.
Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje shine ya sanar da hakan a yammacin ranar Talata, yayin da yake jawabi a wurin taron bikin kaddamar da asibitin da aka gudanar a harabar sa a cikin garin Rano.
KARANTA ANAN: Sanatoci Sun Yi Gum Da Batun Tsige Shugaba Buhari Bayan Dawowar Su Daga Hutu
Yace gwamnatin kano tun bayan samar da masarautu biyar da tayi ta dauki aniyar samar da asibitocin kwararru a daukacin masarautu biyar na jihar nan da nufin saukakawa mazauna garuruwa da kyaukan jihar kano hanyar samun kulawar jami’an lafiya yadda ya kamata kuma akn lokaci.
Da yake jawabi Sarkin Rano Alhaji Kabiru Inuwa ya godewa gwamnatin kano bisa kokarin inganta harkokin kiwon lafiya a masarautar.
Sarkin na Rano ya kuma yi kira ga al’umar masarautar da suyi kyakykyawan amfani da damar da suka samu ta wannan asibi da a cewar sa tazo dai dai lokacin da mazauna yankin ke bukatar karuwar kwararrun jami’an kiwon lafiya don rage kalubalen da suke fuskanta.
A wani labarin kuma: Rundunar Yan Sanda Za Ta Gurfanar Da Dan Chinan Da Ya Kashe Ummita A Kotu
Rundunar yan sandan jihar Kano ta ce za ta gurfanar da Dan Chinan nan Mr Gheng Quanrog gaban Kotu bisa zarginsa da kashe Ummukulsum da aka fi Sani da Ummita.
Idan za a iya tunawa Mista Quanrong ya bi Ummukhulsum ne har gidan iyayenta ya caccaka mata wuka, wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwarta, a ranar Juma’ar da ta gabata.