Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya tabbatarwa da takwaransa na jihar Ekiti, Dr Kayode Fayemi goyon bayansa wajen ganin an tabbatar da aniyarsa ta zama shugaban kasa.
Ya kuma kara da cewa tsawon lokacin da Fayemi ya dauka yana hidimtawa jama’a, yanzu ne ya kamata ace su biya shi ta hanyar goya masa baya.
Mista Femi Ige, wato mai magana da yawun kungiyar Kayode Fayemi Campaign Organisation, ya bayyana hakan a wata sanarwa a yau Juma’a a Abuja, cewa Ganduje ya ba da tabbacin ne lokacin da tawagar yakin neman zaben Fayemi suka ziyarce shi.
Fayemi ya tsaya takarar shugaban kasa a zaben 2023 a karkashin jam’iyyar (APC).
Ige ya ce Ganduje, wanda mataimakinsa, Dr Nasiru Gawuna ya wakilta, ya amince da kwarewar Fayemi na gina fahimtar juna, ilimi da kuma halayen jagoranci na gari.
Gwamnan ya ce yadda Fayemi ke gudanar da ayyukansa da kuma yadda ya jagoranci ya bayyana ga kowa, a don haka zai dace da zama shugaban kasa wanda kuma za ayi alfahari da shi.