Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya bude cibiyar kula da yara masu larurar Tamowa, a yau wadda aka samar a karamin asibiti na unguwa uku a karamar hukumar Tarauni.
Kungiyar likitoci ta kasa da kasa ce ta samar da wannnan cibiya da nufin kula da yaran da ciwon Tamowa ya kama wadanda yawan su ke karuwa kowacce rana.
Taron bude cibiyar dai wani bangare ne na makon lafiya na jihar Kano dake ci gaba da gudana wanda aka fara gudaarwa kwanaki uku da suka gudana.
KARANTA ANAN: Zamfara: PDP Ta Zaɓi Ranar Sake Zaɓen Fidda Gwanin Yan Takarar Gwamna
Da yake jawabi gwamna Ganduje ya yabawa kungiyar bisa kokarin da tayi na samar wannan cibiya da yace zata taimaka wajen samar yara masu lafiya a karamar hukumar Tarauni da ma jihar kano baki daya.
Gwamnan ya kuma yi kira ga al’umar wannan karamar hukuma da su yi kokarin amfana da wannan cibiya tare kuma da sa ido kan bata gari da ka iya amfani da cibiyar wajen fakewa suyi shaye shayen miyagun kwayoyi.
Anasa jawabín kwamishinan lafiya na jihar kano Dr. Aminu Ibrahim Tsanyawa ya bayyana cewa gwamnatin kano a shirye take tayi aiki kafada da kafada da duk masu son ci gaba jihar nan musamman ta fuskar kiwon lafiya.
A wani labarin a kuma: Dalibai Za Su Wadata Da Tallafin Karatu Idan Na Zama Shugaban Kasa – Kwankwaso
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi alkawarin bayar da tallafin karatu ga daliban Najeriya a matakai daban-daban na ilimi idan aka zabe shi shugaban kasa a 2023.
Kwankwaso ya bayyana hakan ne ta shafin sa na Twitter da aka tabbatar a ranar Laraba yayin da yake ba da labarin tayin ilimi kyauta da ya bayar lokacin yana gwamnan jihar Kano.