A yammacin ranar Talata ne gwamnatin jihar Kano ta kira wani taro da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) na jami’o’in jihar guda biyu da ke jihar tare da bukatarsu dangane da dakatar da yajin aikin da suke yi.
Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa taron ya gudana ne tsakanin jami’an gwamnatin jihar da ‘yan kungiyar ASUU daga Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Kano (KUST), Wudil, da Jami’ar Yusuf Maitama Sule (YUMSUK).
Taron wanda ya dauki tsawon sa’o’i da dama ya kawo karshe cikin rashin jituwa tare da yin alkawarin sake haduwa nan da mako guda amma babu tabbacin hakan.
KARANTA ANAN: Kungiyar Kiristoci Ta Jaddada Ƙin Amincewarta Da Tsarin Yan Takara Musulmai
Shugaban ma’aikatan gwamnatin jihar Kano, Usman Bala Muhammad ya roki kungiyar har ma ya bukaci shugabanninsu da su sanya baki domin dakatar da yajin aikin da kungiyar ta ASUU ke yi.
Ya ce duk da haka, ya bai wa ƙungiyar mako guda don sake duba game da kudirin da kuma sake yin taro yayin da yake ba su tabbacin basu hadin kai daga ɓangaren gwamnati.
A wani labarin kuma: Cutar Ƙyanda Ta Kashe Mutane 190, An Samu Mutane 422 Da Jabun Katin COVID-19
Darakta-Janar na Cibiyar Yaki da Cututtuka ta Najeriya (NCDC), Ifedayo Adetifa, ya ce mutane 18,577 ne aka tabbatar sun kamu da cutar kyanda da kuma mutuwar mutane 190 a cikin mako na 35 a jihohi 36 da babban birnin tarayya.
Ya bayyana hakan ne a Abuja jiya yayin taron ministoci da sabbin bayanai kan cutar COVID-19 da ci gaba da aka samu a bangaren kiwon lafiya.
A yayin taron ya samu wakilcin shugaban sashin bayar da amsa, sashen bayar da agajin gaggawa na kiwon lafiya a NCDC, Dokta Olaolu Aderinola, ya ce: “Akwai kananan hukumomi 40 da suka kamu da cutar. Muna ci gaba da tallafa wa jahohi game da barkewar cutar kyanda.”