Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje OFR ya halarci wani Taron Lakca na masarautar Kano, Mai taken: Masarautar Kano, a jiya, Yau da kuma Gobe” da ya gudana a babban dakin taro, a sabon ginin jami’ar Bayaro dake Kano.
Taron na daya daga cikin aiyukan taya murna, da kuma kaddamar da sabbin ma’aikatan Masarautar Mai Martaba sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, a matsayin Sarkin Kano na goma sha biyar.
Kazalika Taron ya sami halartan Mai Alfarma sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubukar na III, da wasu Sarakunan Gargajiya da suka fito daga jihar Kano, da kuma wasu sassan dake fadin kasar nan.
KARANTA WANNAN LABARIN: Buhari ya jajantawa iyalan Dan majalissar jihar Zamfara
Farfesa Abdallah Uba Adamu ne, ya gabatar da makala a wurin taron lakcan.
Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Ganduje, ya sami rakiyar Mataimakinshi, Dakta Nasiru Yusuf Gawuna, Sakataran gwamnatin jihar Alhaji Usman Alhaji, da Honarabul Ali Haruna Makoda, da Daraktan Gangamin gwamnan jihar, Nasiru Aliko Koki, da Kwamishinoni, da wasu manyan jami’an gwamnatin jihar.