• Gwamna Ganduje ya ziyar bikin, ne da ya gudana a birnin Badun dake jihar Oyo.
• Ganduje ya bai Yana Marigayi Abiola a matsayin abun koyi ga yan baya, kuma wanda ya daga darajar jihar Oyo.
• Ganduje ya halarci wurin ne tare da matar shi, da kuma wasu masu ruwa da tsaki dake jihar Kano.
Mai girma gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje OFR da Matar shi Farfesa Hafsat Abdullahi Umar Ganduje, sun halarci wurin tuna wa Marigayi Sanata Abiola Adeyemi Ajimobi, wanda kuma shine tsohon Gwamnan jihar Oyo.
Taron Wanda ya gudana a babban dakin taro na Kasa da kasa dake birnin Badun na jihar Oyo, an shirya shine domin tunawa da marigayi Sanata Abiola Adeyemi.
Lokacin da ya ke jawabi a wurin taron, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana marigayi Ajimobi, a matsayin me kishin kasa da kuma son dorewar Nijeriya.
Gwamnan ya kara da cewa, Marigayi ya kasan ce, wani abun koyi a shekarun 8 da ya kwashe akan mulkin gwamnan jihar Oyo. Inda ya ce, ya kara daga Martaban jihar” inji Gwamna Ganduje.
KARANTA WANNAN LABARIN: An yanke wa Wanda ya kashe bakar fatan hukunci a Amurika
Gwamnan Ganduje ya halarci wurin.ne, tare da Shugaban Jam’iyar APC na jihar Kano Alhaji Abdullahi Abbas, Babban Daractan ganganmin Gwamna Ganduje, Alhaji Nasiru Aliko Koki, Kamishinan Al’adu na jihar Ibrahim Ahmed Karaye, da Shugaban hukumar KNUPDA, Arch Sulaiman Abdulwahab da kuma sauran masu ruwa da tsaki na jihar.
Comments 1