Mai Girma Gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR ya kaddamar da Babban Taro na farko na Gidauniyar Jagoran Mata da Matasan Arewa.
An gudanar da taron ne a Hotel ɗin Niima da ke karamar hukumar Nassarawa a cikin babban birnin jihar.
A nasa jawabin, Gwamna Ganduje ya ce irin wannan gidauniyar za ta taimaka wajen magance matsalolin da ke addabar mata a kasar nan.
Gwamnan ya kara da cewa tabbatar da ganin yadda mata suka kara shiga harkokin mulki a matakin kananan hukumomi ya umurci kowace karamar hukuma ta samu gurbi uku na mata kansiloli da mukamai biyu na mata masu ba da shawara.
DUBA WANNAN LABARIN: Masu Garkuwa Da Mutane sun saki wasu dalibai bayan biyan kudin Fansa 6M
Da take jawabi a wajen taron, babbar jami’ar Gidauniyar ta ƙasa, Hajiya Aishatu Isma’il, ta ce gidauniyar tana aiki ne domin ganin ta bayyana damuwar matan a bangarori daban daban.
Tun da farko, a nata jawabin, kwamishinar harkokin mata, ta jihar Kano Dr Zahra’u Muhammad, ta ce manufar bullo da wannan gidauniya na da matukar amfani don taimakawa wajen tabbatar da bayar da kulawar da ta kamata ga mata.

Ta kuma ce gwamnatin Abdullahi Ganduje ta bullo da shirye-shirye daban-daban don inganta rayuwar mata a jihar.
Gwamnan ya samu rakiyar kwamishinan yada labarai na jihar, Comrade Muhammadu Garba, shugaban jam’iyyar APC, Abdullahi Abbas, Arc. Aminu Dabo, da sauran dattawan jam’iyyar da jami’an gwamnati.