By Abbas Yakubu Yaura
Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya kaddamar da mambobin kwamitin zartarwa na kananan hukumomi 432 na jam’iyyar APC daga mazabar Kano ta Kudu, a wani bangare na shirye-shiryen gudanar da babban taron jam’iyyar na kasa da ke tafe.
Shiyyar ta kunshi kananan hukumomi 16 da mambobin kwamitin zartarwa 4,644 daga gundumomi mazabu 172.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaran gwamnan, Abba Anwar ya fitar ranar Lahadi.
A cewar Anwar, taron ya gudana ne a filin wasa na AA Rano da ke garin Rano a ranar Asabar, inda aka kaddamar da dukkan zababbun shugabannin jam’iyyar daga kananan hukumomi 16 da 172 na shiyyar.
“Shiyyar Sanatan Kano ta Kudu tana da kananan hukumomi fiye da sauran shiyyoyin Sanatocin guda biyu. Tana da kananan hukumomi 16 da unguwannin mazabun siyasa 172.
“A kowace karamar hukuma muna da zababbun shugabannin jam’iyyar guda 27. Don haka kuma a kowace shiyya daga cikin 172, muna da zababbun shugabannin jam’iyyar guda 27,” inji gwamnan.
Sannan ya ci gaba da cewa, “Abin da muke cewa shi ne, an gudanar da zabukan shugabannin jam’iyyarmu a dukkan unguwanninmu da kananan hukumominmu wadanda suka sa kuka zama shugabannin jam’iyyar a wadannan matakai.
Kazalika gwamnan ya taya su murnar samun nasara a zabukan da suka yi da kuma a kotu, inda ya jaddada cewa, “APC a Kano ba ta da adawa a yanzu. Dole ne ku yi aiki tukuru don ci gaban jam’iyyar.”
Sanarwar ta ce Gwamna Ganduje ya kuma raba motoci guda 16 ga shugabannin jam’iyyar na kananan hukumomi 16 da kuma guda daya ta shugaban shiyyar, wanda ya ce wani mai biyayya ga jam’iyyar ne ya bayar.