Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje a ranar Litinin ya karbi bakuncin mahalarta cibiyar nazari kan dabarun jagoranci (NIPSS) karo 44 (rukuni na 3) a gidan gwamnati.
Da yake jawabi yayin wani zama na tattaunawa da mahalarta taron na cibiyar, Gwamnan wanda ya samu wakilcin mataimakinsa Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ya bayyana taken kwas din:
“Karfafa gudanar da mulki a Najeriya – kalubale, zabi da dama” kamar yadda ya dace kuma a kan lokaci.
A cewarsa gwamnatin sa ta himmatu wajen tabbatar da gaskiya da rikon amana, shi ya sa tana cikin jihohin da ke baiwa kananan hukumomi ‘yanci don gudanar da ayyukansu kasancewar matakin kusa da jama’a ne.
“A kokarin samar da shugabanci na gari mun inganta harkokin kananan hukumomi a jihar ta hanyar inganta tsarin kula da lafiya matakin farko na ilimi kyauta da wajibi”.
“Wadannan tsare-tsare sun rage adadin yaran da ba sa zuwa makaranta sosai yayin da yawan daliban makarantunmu ya karu da fiye da kashi 100 cikin 100 da ya ce.”
Gwamnan ya kuma bayyana cewa, ziyarar karatu da aka saba yi a jihar Kano da mahalarta taron daga NIPSS ke yi ya nuna amincewa da nasarorin da cibiyar ta samu a jihar.
Tun da farko, Shugaban tawagar Birgediya Janar Chukwuemeka Udaya mai ritaya ya ce shugaban yana baiwa cibiyar duk abubuwan da suka kamata, don gudanar da bincike a bangarori da dama.
Sakataren yada labaran mataimakin Gwamnan Hassan Musa Fagge a wata sanarwa da ya fitar ya rawaito yadda shugaban ya yabawa gwamnatin jihar Kano bisa bada izinin ziyarar da aka yi musu da kuma karramawar da aka yi musu.