Gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR, ya jagoranci kaddamar wa tare da mika takardun kama aiki ga wakilan Hukumar gudanarwa da harkokin Majalisar Dokoki ta jiha.
Gwamnan Ganduje ya kaddamar da Hukumar ne yayin zaman majalisar Zartarwa na mako-mako na musamman, tare da Maitamakin sa, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, da Sauran kwamishinoni da yan majalisar zartawa, wanda aka gudanar a dakin taro na Africa House, dake Gidan Gwamnati.
Gwamnan ya ce, yana da kwarin gwiwar cewar, wakilan Hukumar za su yi aikin su yadda yakamata, ta yadda majalisar za ta gudanar da ayyukan ta yadda yakamata, wajen gudanar da harkokin ta na yau da kullum.
Hukumar na karkashin Shugancin Alhaji Nasiru Mu’azu Kiru da mataimakin sa Hon. Ishaq Tanko Gambaga da sauran mambobi Takwas.
Ka’ida na wa’adin Shugabancin Hukumar da wikilan ta shine shekara hudu.
Comments 1