By Abbas Yakubu yaura
Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya naɗa Alaramma Ahmed Sulaiman a matsayin kwamishina na biyu a hukumar kula da ilimin makarantun firamare ta jihar Kano.
Gwamnan ya kuma mikawa Sheshin Malamin takardar shaidar Kama Aikin ne a Gidan Gwamnatin Jihar Kano a gaban Shugaban Kungiyar Izala na Kasa Sheikh Abdullahi Bala Lau da Sakataren sa Sheikh Kabiru Haruna Gombe.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Gwamnan yace ya nada Malam Ahmad Sulaiman a matsayin Kwamishinan na biyu saboda irin Gudunmawar daya dade yana bayarwa a wajen cigaban ilima da harkokin addinin Musulci a Jihar Kano.
Sannan ya Kuma bukace shi daya zamo Mai cigaba da bada Gudunmawar don bunkasawa tare da inganta harkokin Ilimi a Jihar Kano Kamar yadda Gwamnatinsa ta kudiri aniyar yin hakan.
Sheshin Malamin Ahmad Sulaiman ya yi addu’ar Allah ya san albarka a wannan kujera daya samu da kuma neman addu’ar jama’a kan Allah ya taya shi riƙo wajen gudanar da aikin sa.