Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya rantsar da sabbin alƙalan babbar kotun jihar guda shida da zummar rage jinkirin shari’o’i.
Gwamnan ya ce ƙarin yawan alƙalan zai kuma taimaka gaya wajen samun adalci da damar sauraron kowane ɓangare a kotunan jihar.
Ya ce dukkannin sabbin alƙalan da aka rantsar sun cancanta, domin sun ci jarabawa tare da samu yabon hukumar kula da Alƙalai (NJC).
Gwamnan wanda ya ce ɓangarori uku na gwamnati a jihar za su yi aiki tare domin amfanin jama’ar jihar, ya buƙaci sabbin alƙalan da su kare mutuncin da aka sansu da shi da na ɓangaren shari’a.
Antoni Janar na Kano, Muhammad Lawan ya ba wa sabbin alƙalan rantsuwar kama aki a ranar Juma’a.
Sabbin alƙalan da suka karɓi ranstuwar su ne: Abubakar Maiwada, Maryam Sabo, Zuwaira Yusuf A, Jamilu Sulaiman, Sunusi Ma’aji da kuma Hafsat Yahaya Sani.