Sakamakon rashin shirya sabon zaɓe bayan karewar wa’adinsu, Gwamnan Jahar Kano, Dr Umar Abdullahi Ganduje ya rusa shugabannin Ƙungiyar ƴan kasuwa, masana’antu, ma’adinai da noma ta Kano, KACCIMA, ba tare da ɓata lokaci ba.
Gwamnan ya fusata kan yadda jami’an zartaswar da aka kora suka yi zaman dirshan, inda ya bada umarnin tsige su cikin gaggawa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Shugabancin Najeriya: Dalilan da suka sanya naƙi ɗaukar Bola Tinubu Abokin Takara ta — Atiku
A cewar wata sanarwa da sakataren gwamnatin Jahar Kano, Alhaji Usman Alhaji ya sanyawa hannu, ya zama wajibi a ɗauki matakin ne saboda gazawar Shugabannin Hukumar na yanzu wajen shirya sabon zaɓe mai karɓuwa tun bayan ƙarewar wa’adinsu.
Sanarwar ta ƙara da cewa, tuni Gwamna Ganduje ya amince da kafa kwamitin ruƙo mai mutane tara, ƙarƙashin jagorancin wani ɗan kasuwa mai masana’antu, Alhaji Lawan Sale Garo.
Sharuɗɗan kwamitin, da dai sauransu, sun haɗa da shirya zaɓe cikin watanni shida, tare da maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali a dukkan ayyukan majalisar.
Sauran ƴan kwamitin sun haɗa da Ambasada Muktari Gashash a matsayin mataimakin Shugaban Ma’aikatar kasuwanci, Dr Salim Saleh Muhammad, Alhaji Yakubu Uba, Alhaji Tijjani Usman, Alh. Kabiru Hamisu Kura, Hajiya Aisha, Sulaiman Baffa, Alhaji Bashir Dado da Bauran Gaya.
Da yake jawabinsa Shugaban kwamitin, Garo ya nuna jindaɗin ga gwamnan bisa amincewar da aka basu tare da bada tabbacin cewa kwamitin zai yi bakin ƙoƙarin sa wajen cimma burin da aka sanya a gaba.