Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya yi wa tsohon gwamnan jihar, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ta’aziyyar rasuwar kaninsa, Kwamared Inuwa Musa Kwankwaso.
Inuwa ya rasu ne a ranar Lahadi kuma an yi jana’izarsa a jiya Litinin.
A wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar Malam Muhammad Garba ya sanyawa hannu, gwamnan ya bayyana rasuwar injiniyan da aka horas da aikin noma a matsayin rashi ba ga iyalansa kadai ba har ma da jiha da kasa baki daya.
Ya bayyana cewa marigayi Kwamared Kwankwaso ya bayyana kansa a matsayin ma’aikaci mai kwazo kafin ya yi ritaya, musamman a lokacin da ya yi aiki a shirin shukar dazuka inda ya kwashe shekaru da dama Yana aiki.
Gwamna Ganduje ya yi addu’ar Allah ya jikan sa rahma ya Kuma Sanya shi a Aljannar Firdausi da daukacin iyalansa baki daya.