Gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR, ya halarci bikin makon Hisbah wanda aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha dake Kofar Mata, karkashin Jagorancin Shugaban Hukumar, Ustaz Muhammad Ibn Sina.
Yayin taron, Gwamna Ganduje ya kaddamar da dakarun sakai na Hisbah su dubu biyar da dari bakwai, tare da chanjawa jamian na Hisbah Uniform, da kuma karin girma ga dukkan jami’an da suka shekara shida suna aiki.
Gwamnan ya yaba da yadda Yan Hisban suke gudanar da aikin su, inda ya ce, za’a duba yiyuwar kara musu albashi.
Yayin taron Gwamnan yana tare da Mataimakin sa, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, da Sakataren Gwamnati Alhaji Usman Alhaji, da Shugaban jam’iyyar APC Alhaji Abdullahi Abbas, da Dattijo Alhaji Nasiru Aliko Koki, da Shugaban ma’aikatan fadar Gwamnati Hon. Ali Haruna Makoda, da Kwamishinoni, da mai bai wa Gwamna shawara akan harkokin addinai, Hon. Alibaba Fagge, da sauran jami’an Gwamnati.
A wani labarin Kuma na daban.
Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR, ya jagoranci bude taron wayar da kai kan da’ar aiki da bayyana kadarori na yini biyu wanda Conde of Conduct Bureau da hadin gwiwar ma’aikatar kananan hukumomi suka shirya karkashin Jagorancin kwaminan ma’aikatar, Hon. Murtala Sule Garo.
Taron wanda aka shiryawa Shugabannin kananan Hukumomi da Kansiloli zababbu da nadaddu da sauran ma’aikatan ma’aikatar kana hukumomin, an gudanar dashi ne a dakin taro na meena dake Lodge Road.
Taron ya samu halartar Mataimakin Gwamna, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna da Sakataren Gwamnati Alhaji Usman Alhaji da shugaban jam’iyyar APC, Alhaji Abdullahi Abbas da kwamishinoni da sauran jami’an Gwamnati.
Comments 1