• Gwamnan dai ya gaji wannan aikin ne daga tsohuwar gwamnatin da ta gabata.
• Nan take gwamna Ganduje ya Umarci kwamishinan aiyuka na jihar da ya binci kundin aikin domin Sannin inda aka tsaya.
• Nan take daruruwan al’umar da ke wurin kuka fara murna da shewa kan alkawarin da gwamnan ya yi
Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya yi alkawarin kammala titin da ya taso daga Jakara zuwa Gorondutse, nan ba da jimawa ba.
Har ma a nan take ya ba da umarni ga Kwamishinan Ayyuka na jihar, da ya yi gaggawar bin takardun aikin, dan ganin a ina a ka kwana, kuma a ina za a tashi.
Ya yi wannan jawabin ne lokacin da ya ke kaddamar da Makon Shirin Tsaftace Birnin Kano, wanda a ka kaddamar a katafariyar kwatar nan ta Jakara, wacce ta zarce har zuwa Kwakwaci, gaban Gidan Jarida na Triumph, jiya Talata.
Titin wanda tsohuwar gwamnatin Rabi’u Musa Kwankwaso ta fara kuma ta watsar ya dade ya na ci wa mutanen yankin tuwo a kwarya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Hadarin mota ya kashe mutun 7 da raunata wasu da dama
Daidai lokacin da Gwamna Ganduje ya yi wannan maganar kammala aikin titin, sai wajen ya dau wata irin sowa daga daruruwan mutanen da su ka je wajen waccan kaddamarwa.
Ya ce “Mun biyo ta wannan titi mai muhimmanci mun ga yadda aikinsa ya kasance. Yanzu haka ina tare da Kwamishinan Ayyuka na Jihar Kano, na kuma ba shi umarnin da ya koma ofis ya dauko fayil din, a ga yadda aikin yake, saboda a yi gaggawar kammala aikin.”
“Wannan titi mai muhimmanci, na Sheikh Mahmud Salga, da ya faro daga kan titin Malam Aminu Kano, Gorondutse, zuwa Jakara bola, za mu tabbatar an kammala shi ba da jimawa ba,” in ji shi.