Mataimakin gwamnan Kano Dakta Nasiru Yusif Gawuna ya zama mukaddashin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, sakamakon yanayin tafiya da ya kamata gwamnan.
Gwamna Abdullahi Ganduje dai zai bar Najeriya ne, don gudanar da wani uzuri na musamman a can, wanda ya shafi aikinsa, matsayinsa na gwamnan.
Sakataren yada labaran Gwamnan Abba Anwar ne ya sanar da hakan a wata Sanarwa, daya aikowa da jaridar Dimokuraɗiyya a yammacin Larabar nan.
Gwamnan Ganduje ya bukaci ma’aikatu da hukumomin gwamnati kan su hada kai da mataimakin nasa, wajen aiki tare kamar yadda suke bashi hadin kai.
Yanzu haka dai Dakta Gawuna shine mukaddashin Gwamnan har zuwa sanda zai dawo, kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa Gawun yanzu haka shine ɗan takarar gwamnan na Jamiyyar APC a zaben 2023, dake tafe, yayin da Murtala Sule Garo ke a matsayin mataimakinsa.