Daga Bashir Abdullahi El-bash:-
A yunƙurin da ya ke wajen ganin an samu nasarar tabbatar da zuwan kowane yaro makaranta da kuma ba da Ilimi kyauta tun daga Firamare har zuwa babbar Sakandire kamar yadda ya fada a baya-bayan nan, gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano, ya kai ga cimma matakin kiran taron masana na musamman nan da wasu ƴan makonni masu zuwa domin tattauna dukkan batutuwa masu alaka da wannan tsari.
Gwamna Ganduje ya bayyana cewa, kwararrun masana kan Ilimi ne za su halarci taron, za kuma su zo da batutuwa da tsare-tsare na zamani kan yadda za mu samu kykkyawan sakamako bayan kaddamar da wannan tsari.
Gwamna Ganduje ya bayyana haka ne jiya a gidan gwamnatin Jihar Kano, ya yin da ya jagoranci wani taron masu ruwa da tsaki kan tabbatuwar zuwan kowane yaro makaranta da kuma ba da Ilimi kyauta. Waɗanda su ka ƙunshi shugabannin sassan Ilimi na Jiha ƙarƙashin ma’aikatar Ilimi ta tarayya da kuma na manyan makarantun gaba da sakandire da wakilcin masarautu biyar na Jihar da kuma sauran masu ruwa da tsaki.
“Dukkanmu mun yi imani Ilimi shi ne ginshiƙin cigaban tattalin arziƙi da samar da ayyukan fasahar zamani, da kuma kauda rashin aikin yi. Taron masana da za mu kira zai taimaka mana wajen samun ingantacciyar nasara da kyakkyawan sakamako kan tabbatuwar zuwan yara makaranta da kuma ba da Ilimi kyauta tun daga Firamare har zuwa babbar Sakandire”. Inji gwamna Ganduje.
“Daga bangaren masana kan wannan babban tsari da mu ka bijiro da shi, akwai wadanda su ke kwararru ne kan Ilimin baidaya, da kuma kwararru kan ilimin lafiya da kimiyya da fasaha, wasu kuma kwararru ne kan ilimin tsarin bindddigi da kuma daidaita harkokin Ilimi wasu kuwa masana ne kan harkokin jarrabawa da kuma masana kan tsarinmu na zamanantar da karatun Allo”. Gwamna ya yi bayani.
Makarantun gargajiya su ma su na da gagarumar rawar da za su taka wajen cimma nasarar da mu ka nufata, shi ya sa mu ka shigo da su.
Sannan su ma kafafen watsa labarai su na da babbar gudunmawar da za su bayar, hakan ne ma ya sanya gwamna Ganduje ya yi kira a gare su da su ba da hadin kai wajen aiki tare don cimma wannan buri.
Ya yin da ya ke gabatar da nasa jawabin, Dakta Kabir Shehu, Shugaban kwamitin tabbatar da zuwan yara makaranta da kuma ba da Ilimi kyauta, ka na kuma Shugaban ma’aikata na Jiha, ya yi tsokaci kan ayyukan da kwamitinsu ya yi tun bayan da gwamna ya ƙaddamar da su a baya, tare da tabbatar da aniyar yin duk mai iyuwa wajen ganin an samu managarciyar nasara.
Ya kuma kara da cewa bayan kammala taron masana, za a fidda taswirar yadda ya kamata ayi wajen tabbatar da cewa kowane yaro ya samu Ilimi kuma kyauta.
Bugu da ƙari kuma, (DFID) da babban bankin tarayya sun yi alƙawarin hada ƙarfi da ƙarfe da gwamnatin Jihar Kano domin samun nasarar wannan tsari.
A wannan karon, mai girma gwamna ya faro tun daga Firamare matakin farko har zuwa babbar sakandire, hakika, wannan babban cigaba ne. Inji Dakta Kabir.