Gwamnan Jahar Abia Okezie Ikpeazu ya rantsar da Kwamishinoni 27 a Umahia a ranar Talata, tare da umartar su dasu bayar da gudummawa wajen bunƙasa wa da cigaban Jahar.
Yace a lokacin bikin rantsarwar cewa, jahar na fama da ƙalubale, kuma tana akan wani yanayi sai dai ikon Allah SWT.
Gwamnan yace sabbin kwamishinonin ana saran zasu zasu bada goyon baya ga gwamnati, a ƙoƙarin ta na inganta kyakkyawar rayuwar Al’ummar Jahar Abia.

KARANTA WANNAN LABARIN: Da ɗuminsa: Gwamnonin Kudu maso yamma na gudanar da taron tsaro a Lagos
Yace Gwamnatin Jahar ta damu wajen ganin ta kammala ayyukan raya ƙasa da take shimfiɗa wa, gami da ƙirƙirar wasu kafin ƙarshen wa’adin mulkin shi.
Gwamnan ya ƙara dacewa Gwamnatin Jahar tana damuwa akan cigaban jahar, Kuma ba zata yi aiki da duk wani da bazaiyi aiki akan haka ba.
Ikpeazu yace Gwamnatin Jahar zata bayar da yanayi mai kyau ga Kwamishinoni, domin gudanar da aikace-aikacen su yadda ya kamata.
Ya buƙaci kwamishinonin dasu maida hankali wajen cigaba, gami da bayar da tsare-tsare da shirye-shiryen gwamnati.
Dayake jawabi a madadin abokanan aikinsa, Kwamishinan Yaɗa Labaru Eze Chikamnayo ya godema gwamnatin Jahar data basu dama domin yiwa al’ummar Abia aiki.
Comments 1