Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana Shirin Gwamnatinsa na amfani da Fasahar Zamani ta hanyar ci gaba da bayen Shanu.
Gwamna Ganduje ya bayyana hakan a Jiya Asabar, a wajen kaddamar da Hujin Shanu da Dabbobi, wanda Shirin kula da noma da kiwo na jihar Kano, ya dauki nauyin gabatarwa Hadin Gwiwa da bankin Islama, Wanda ya lakume kudi sama da Naira miliyan 103.
Taron dai ya gudana ne a cibiyar kiwo ta Hukumar bunkasa Noma da kiwo dake Kadawa a karamar Hukumar Garin Malam, tuni dai aka Samar da bijiman shanu Waɗanda darajarsu ta Kai sama da Naira miliyan 9, da niyyar bayen shanu akalla 25,000 a shekara.
A yayin bikin wanda ya samu halartar manyan masu ruwa da tsaki a harkar kiwo da suka hada da kungiyoyin makiyaya, Gwamna Ganduje ya bayyana cewa, wannan na daga burin ganin an inganta shanun na gida, ta yadda za a inganta kudaden shigar makiyayan da Kuma rage ya kalubalen da suke fuskanta.
Gwamnan ya ce gwamnatinsa na inganta harkokin bayen shanu a matsayin wani bangare na yunƙurin canzawa kiwo irin na gargajiya Zuwa kiwo irin na zamani don inganta harkokin tattalin arziki, kamar yadda ake yi a duniya.
Wakilinmu Ibrahim Hassan Hausawa ya rawaito Mana cewa Gwamnan, ya godewa Bankin Raya Musulunci da Asusun inganta Rayuwa na LLF, sakamakon irin gudunmawar da suka bayar wajen tabbatuwar wannan tsari.